Yayin da yake jawabi ga sojojin ƙasar ranar Juma’a a wata ziyara da ya kai jihar Katsina, ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ƴan fashin daji, shugaban ƙasar ya ce matsalar ƴanta’adda da masu garkuwa da mutane da ƴan fashin daji ta jima a ƙasar.
“Ƴan Najeriya sun zuba muku ido, suna jiran ku kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da ƙwato kowane yanki na ƙasarmu, ku nuna wa maƙiyan Najeriya cewa ƙaryarsu ta ƙare”, in ji Shugaba Tinubu.
”Gwamnati na ɗaukar matakan samar muku isassun kayan aiki, da suka haɗ da sabbin fasahohin zamani da sabbin hanyoyin tattara bayanan sirri da dabarun yaƙi, ba wai don kare ƙasarmu kaɗai ba, sai don samun ƙarfin da za ku iya murƙushe duk wata barazana a ko’ina ta ɓulla”.
Dakarun Najeriya na yaƙi da Boko Haram tun 2009, inda suka samu nasarar karya logon ƙungiyar ta hanyar kashe manyan kwamandojinta. To sai dai a baya-baya nan, ƙungiyar tsagin ISWAP na nuna alamun dawowa da ayyukansu a wasu sassan ƙasar, musamman arewa maso gabashi.
Haka kuma akwai ƙaruwar ayyukan masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a wasu sassan shiyyar arewa maso yammaci, ciki har da Katsina da yake ziyarar, inda suke kashe mutane tare da ƙona ƙauyuka da garuruwa.
Rahoto BBC Hausa