Wani Ɓangare Na Jawabin Shugaba Tinubu Ga Dattawan Jihar Katsina.

 

“Game da batun tsaro da tsohon gwamna Aminu Bello Masari ya bijiro da shi, eh, na amince cewa matsalar tsaro babban kalubale ne ga kasar nan. Na yi wa jami’an sojoji jawabi daga isowa ta ɗazu, na kuma tabbatar musu cewa za mu yi duk mai yiwuwa domin yaƙar ta’addanci da ganin bayan ‘yan bindiga.

“Za mu ƙara zuba maida hankali a fannin fasaha, sannan za mu karɓe iko da dukkan dazuka. Lamarin Tsaro batu ne na ƙasa baki ɗaya, ba na gari ko yanki kadai ba. Idan har da gaske muke wajen jawo masu zuba hannayen jari a Najeriya, to dole ne mu magance matsalar tsaro.

“Ƴan kasuwa ba sa son asara, zuba jari ba zai yiyu a inda ake fama da ‘yan bindiga da ta’addanci ba. Za mu warware wannan matsala tare da haɗin kan jihohi da kuma ƙananan hukumomi,” in ji shi.

Shugaba Tinubu ya kuma tabbatar da cewa waɗanda matsalar tsaro da ta’addanci ya shafa za su samu tallafi na musamman domin domin farfado da rayuwarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SUBSCRIBE US

It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution

Copyright BlazeThemes. 2023