Tinubu Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinonin INEC da Mambobin Hukumar Ladabtar da Ma’aikata

 

Shugaban Kasa Ya Bukaci Sabbin Jami’ai Su Rungumi Gaskiya da Karfafa Gwamnati.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin da rana, ya rantsar da sabbin kwamishinonin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kuma sabbin mambobin Hukumar Ladabtar da Ma’aikata a fadar gwamnati da ke Abuja.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin rantsarwar, Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin jami’an da su kasance masu rikon gaskiya da kwazo wajen gudanar da ayyukansu.

“Ina kira gare su da su rungumi gaskiya da kwarewa a cikin ayyukansu, tare da bayar da gudunmawa wajen bunkasa wadannan hukumomi guda biyu,” in ji Shugaba Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SUBSCRIBE US

It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution

Copyright BlazeThemes. 2023