Tinubu ya nada sabbin Kwamishinoni a hukumar Zabe INEC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Abdulrazak Tukur Yusuf a matsayin kwamishina na ƙasa a hukumar zabe mai zaman kanta ta (INEC) mai wakiltar Arewa maso Yamma.

Shugaban ya kuma nada wata lauya mai suna Saseyi Feyijimi Ibiyemi a matsayin kwamishiniyar zabe (REC) mai wakiltar jihar Ondo.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanugamai ya bayyana hakan ne a wata sanarwa jiya litinin.

 

Sanarwar ta kara da cewa, “Tukur, mai shekaru 59, yana da digirin digirgir a fannin fasaha daga jami’ar Bayero, da difloma a fannin tattalin arziki daga jami’ar Bradford ta kasar Ingila da kuma babban digiri na biyu daga jami’ar Leeds, ita ma a kasar Ingila.

 

“Ya fara aiki da INEC a shekarar 1999 a matsayin mataimakin babban jami’in gudanarwa kuma ya zama daraktan ayyuka da dabaru na zabe.”

 

Onanuga ya kuma ce idan majalisar dattawa ta wanke Ibiyemi za ta maye gurbin wani lauya mai suna Niyi Ijalaye wanda ya rasu a watan Agusta a lokacin da yake rike da mukamin kwamishinan zabe a jihar Ogun.

 

“Ibiyemi, mai shekaru 58, wadda ta fito daga Ilaje a jihar Ondo, a halin yanzu ita ce sakatariyar gudanarwa na INEC a jihar Legas.

 

“Ta sauke karatu daga Jami’ar Obafemi Awolowo a 1987 kuma ta zama cikakkiyar lauya a 1988, in ji sanarwar.

Tukur ɗan asalin jihar Katsina ne, Fejiyemi kuma ‘yar asalin jihar Ondo ce, ana sa ran majalisa za ta tantance su nan ba da jimawa ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SUBSCRIBE US

It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution

Copyright BlazeThemes. 2023