Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ɗaukar matakan da suka dace domin samar da zaman lafiya da tsaro a matsayin ginshiƙan cigaban ƙasa nan masu ɗorewa.
Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai Malam Rabiu Ibrahim, ya faɗa a sanarwa ga manema labarai cewa Idris ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, yayin jawabin sa na farko a matsayin Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Gidauniyar Cigaban Jihar Neja (NSDF), wadda wata ƙungiya ce ba ta siyasa ba da ke bayar da shawarwari don kawo cigaban jihar.
Idris ya ce babu yadda za a yi a samu cigaba idan babu zaman lafiya da tsaro, ya ƙara da cewa abu ne wanda Shugaba Tinubu ya fahimta sosai, kuma gwamnatin sa tana baƙin ƙoƙari matuƙa a wannan fage a wani ɓangare na gagarumin tsarin da take bi don sauya fasalin ƙasar nan.
Ya ce: “Zan yi amfani da wannan damar in jaddada alaƙar da ke tsakanin cigaba, zaman lafiya, tsaro da kuma ababen more rayuwa. Waɗannan abubuwa suna da alaƙa da juna, kuma suna ƙarfafa juna. Ba za a iya samun cigaba mai ma’ana ba idan babu zaman lafiya da tsaro, haka kuma amfanin cigaba kan kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan wata haƙiƙa ce da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya fahimta sosai, wanda ya sa gwamnatin sa ke zuba jari sosai a waɗannan fannonin a matsayin wata dabarar da za ta sauya fasalin ƙasa gaba ɗaya.”
“Mai girma Shugaban ya bayyana ƙarara cewa babu zaɓi a batun tsaro; shi ne ginshiƙin da ke ɗauke da duk sauran abubuwa na cigaban ƙasa. Hakan ne ya sa, a ƙarƙashin jagorancin sa, Gwamnatin Tarayya ta dage, ba kama hannun yaro, wajen ƙarfafa hukumomin tsaron mu. Manufar haka a bayyane take: a samar da yanayin da ya dace inda al’umma za su haɓaka, harkokin kasuwanci su inganta, kuma cigaba ya kafu sosai.”