A ƙoƙarinsa na magance matsalar fitar ƙwararrun masana kiwon lafiya ƴan Najeriya zuwa ƙasashen waje yin aiki, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a fidda Naira Biliyan 110 a matsayin tallafi ga jami’o’i 18 da aka zaɓa a faɗin ƙasar.
Shirin wata manufa ce ta kyautata ilimin lafiya gami da bunƙasa ingancin jami’o’i su riƙa samar da ƙwararrun masana kiwon lafiya, kamar yadda Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Kowace jami’a ɗaya za ta samu kuɗaɗen da yawansu ya kai Naira Biliyan 4 da kuma Naira miliyan 750 da aka ware musamman domin gina gidajen kwanan ɗalibai. Za kuma a yi amfani da kuɗaɗen wajen samar da manyan ɗakunan gwaje-gwaje na zamani guda guda 8 waɗanda za a raba su a shiyoyin ƙasar a wani mataki na faɗaɗa shirye-shiryen kiwon lafiya.
Jami’o’in da za su ci gajiyar tallafin sun haɗa da:
1. Jami’ar Nnamdi Azikwe (Nnamdi Azikiwe University)
2. Jami’ar Jihar Bayelsa, (Bayelsa State University)
3. Jami’ar Legas, (University of Lagos)
4. Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (Ahmadu Bello University)
5. Jami’ar Benin (University of Benin)
6. Jami’ar Imo (Imo State University)
7. Jami’ar Ibadan (University of Ibadan)
8. JAmi’ar Kimiyya Ta Ondo (University of Medical Sciences, Ondo)
9. Jami’ar Benue (Benue State University)
10. Jami’ar Ƴar’adu’a (Umaru Musa Yaradua University)
11. Jami’ar Nsukka (University of Nigeria, Nsukka)
12. Jami’ar Kalaba (University of Calabar)
13. Jami’ar Tafawa Ɓalewa (Abubakar Tafawa Balewa University)
14. Jami’ar Jos (University of Jos)
15. Jami’ar Ilorin (University of Ilorin)
16. Jami’ar Jihar Gombe (Gombe State University)
17. Jami’ar Ɗanfodio (Usmanu Danfodio University)
18. Jami’ar Maiduguri (University of Maiduguri).
Tallafin zai kuma yi amfani wajen gudanar da ayyuka a makarantun lafiya ta hanyar gyara ɗakunan ɗaukar darasi, zamanantar da ɗakunan gwaje-gwaje na kimiyya, gami da kyautata harkokin koyo da koyarwa.
Ana kuma sa ran shirin zai taimaka wajen samar da ƙarin ƙwararrun likitoci, ma’aikatan jinya, likitocin haƙori gami da gogaggun masana magunguna da za su taimakawa fannin kiwon lafiyar ƙasar.