Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gaggawa ga Sufeto Janar na Ƴan Sanda, Kayode Egbetokun, da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, da su gaggauta kama makasan mutane sama da 100 da aka kashe a harin da wasu ƴan ta’adda suka kai a ƙauyen Yelewata na jihar Benuwe.
Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa da manyan shugabannin jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar Benuwe da ke Markudi. Taron ya haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, tsoffin gwamnonin jihar, sarakunan gargajiya, da kuma gwamnonin jihohin Kwara, Imo, Kogi, Plateau, Ondo da Nasarawa.
A jawabin da ya gabatar, Shugaba Tinubu ya bayyana rashin jin daɗinsa kan rashin kama dukkan waɗanda suka aikata kisan gillar.
“Ta yaya babu wanda aka kama har yanzu dangane da wannan mummunan kisa da aka yi a Yelewata? Sufeto Janar, ina waɗanda aka kama? Dole ne a kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa cikin gaggawa.”
Shugaban ƙasar ya kuma umurci shugabannin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA) da su ƙara zage damtse wajen tattara bayanan sirri domin cafke masu laifin.
Ya kuma shawarci Gwamna Hyacinth Alia da ya kafa wani kwamiti na zaman lafiya da zai ƙunshi tsoffin gwamnonin jihar, dattawa, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati daga tarayya, da kuma ’yan wasu jihohin da ke zaune a Benuwe.
“Mu sake haduwa a Abuja domin tsara yadda za a tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa. A shirye nake nayi dukkan abinda zai yiwu dan samun zaman lafiya. Na yi muku alkawari, za mu samu zaman lafiya. Za mu sauya wannan masifa zuwa wata dama ta samar da ci gaba,” in ji Shugaba Tinubu.
Ya kuma buƙaci Gwamna Alia da ya ware wani sashe na ƙasa a jihat domin kiwon dabbobi cikin tsari na zamani, tare da umartar Ministan Aikin Noma da Tsaro na Abinci da ya bibiyi lamarin.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya bukaci mutane su bada agajin jini ga waɗanda ke jinya a Asibitin Koyarwa na Jihar Benuwe, inda ya ziyarci waɗanda suka jikkata da kuma ma’aikatan asibiti.
A yayin ziyarar, Ya bayyana cewa:
“Nazo nan ne domin na kaddamar da ayyukan raya ƙasa, ba don ganin fuskoki dake cike da bakin ciki ba. Amma tabbas. babu ci gaba sai da zaman lafiya.”
“Rayuwar ɗan adam tafi darajar shanu. Mun zo mu yi gwamnati ne don mu kula da mutane, ba don mu binne su ba.”
Shuagaba Tinunu Ya ƙarfafi Gwamna Alia da ya tabbatar da dawo da zaman lafiya a jihar.
“An zaɓe ka a ƙarƙashin jam’iyyar ci gaba don ka samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ba don ka rika binne mutane da ta’aziyya ga matan da mazajensu suka rasu ba. Za mu yi aiki tare da kai don cimma wannan zaman lafiyar, kuma dole kai ma kayi aiki damu”
A nasa jawabin, Gwamna Hyacinth Alia ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta kafa asusun tallafi na musamman ga al’ummomin da rikicin ya shafa a jihar. Ya ce hakan zai taimaka wajen sake gina gidaje, ababen more rayuwa da kuma dawo da hanyoyin samun abin rayuwa ga manoma da sauran al’umma.
Sarkin Kabilar Tiv kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar Benuwe, Tor Tiv, Farfesa James Ayatse, ya yaba wa Shugaban Ƙasa bisa ziyararsa ta jinya ga waɗanda suka jikkata, inda ya ce Tinubu ne Shugaban Ƙasa na farko da ya kai irin wannan ziyarar kai tsaye bayan irin wannan mummunar harin.
“Ba rikicin makiyaya da manoma bane, ba rikicin ƙabilanci bane, ba ramuwar gayya ba ce. Wannan wani shiri ne na gangan, na kisan kare dangi da kwace ƙasar jama’a da ake aiwatarwa ta hannun ’yan ta’adda.” Inji shi.
Ya bukaci Shugaban Ƙasa da ya fahimci ainihin yanayin matsalar tare da mayar da hankali wajen dawo da zaman lafiya a Benuwe da Najeriya baki ɗaya.
“Kada a bar mu cikin kuka da bakin ciki. Ka dawo mana da zaman lafiya a jihar Benuwe, domin manomanmu su koma gonakinsu, su cigaba da ciyar da ƙasa da abinci.”