A yau ne Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu wanda
Mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilta ya sake kaddamar da sabon tit a garin Abuja.
Aikin titin wanda ya taso tun daga Obafemi Awolowo Way a Jabi ya haɗa da sauran hanyoyin gundumar ɗaki biyu.
Kazalika sabuwar hanyar ta haɗa hedikwatar hukumar ‘yan sanda da babbar kotun tarayya da ke Jabi da hedikwatar kotun ɗa’ar ma’aikata, da sabon sashin kotun ɗaukaka ƙara na babban birnin tarayya Abuja.
Aikin titin da gwamnatin babban birnin tarayya ta aiwatar na daga cikin ƙoƙarin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke yi na inganta ababen more rayuwa da hanyoyin sadarwa a babban birnin tarayya da ma ƙasa baki ɗaya.