Sauye-sauyen Gwamnatin Tinubu na Shekara Biyu Shaida ce ta Jagoranci Mai Hnagen Nesa – Minista Mohammed Idris

 

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai ga Al’umma, Mohammed Idris, ya bayyana cewa nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu cikin shekara biyu kacal sun zama shaida ta gaskiya na jagoranci mai hangen nesa da jarumtaka.

Da yake jawabi a wajen taron farko na Tattaunawar Kasa kan Shiga Al’umma cikin Harkokin Gwamnati da Tsaron Kasa da aka gudanar a Abuja, Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da sauye-sauye da manufofi na musamman da suka fara haifar da gagarumin sakamako. Daga cikin manyan nasarorin da ya jero akwai cire tallafin man fetur, kawar da damfara a kasuwar musayar kudade, gina manyan hanyoyi, tsarin ba da rance ga dalibai, kafa CreditCorp, da kuma samar da Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya.

Idris ya ce wadannan matakai suna farfado da amincewar jama’a ga gwamnati, suna saukaka farashin abinci, inganta tsaro, da kuma samar da ingantacciyar gwamnati har zuwa matakin kananan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SUBSCRIBE US

It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution

Copyright BlazeThemes. 2023