Rikici ya kunno kai a Kwankwasiyyar Kano

Alamu na nuna cewa wata rigima ta tashi a gidan siyasa na Kwankwasiyya wadda ke jan ragamar mulkin Kano karkashin jam’iyyar NNPP.

 

Tun a jiya ne dai wasu jiga jigai da ke da mukamin wakilan Tarayya na Dala da Rano/Bunkure/Kibiya suka ayyan ficewa daga tsarin na Kwankwasiyya kuma suka nemi gwamna Abba Kabir Yusuf da ya Tsaya da Kafarsa, watau ya rika yin gaban kansa ba tare da umarnin Madugun Kwankwasiyyar Rabiu Musa Kwankwaso ba.

 

Masu nazarin siyasa na ganin hakan ba ya rasa nasaba daga irin yadda ake ganin Madugun ya mamaye al’amuran gwamnati kuma hakan ya fito fili a fitar da ‘yan takara na  zaɓen kananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar 26 ga Oktoba 2024.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SUBSCRIBE US

It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution

Copyright BlazeThemes. 2023