Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana haka bayyana haka ne a saƙon godiya da ya aika wa mahalarta taron farko da aka yi da ‘yan jaridun soshiyal midiya na Arewacin Najeriya a ranar Laraba a Abuja.
Ya bayyana jin daɗinsa kan yadda taron ya gudana, inda aka samu musayar ra’ayoyi da shawarwari masu amfani daga mahalarta. Ministan ya jaddada cewa irin wannan zaman za a ci gaba da gudanar da su kafin ƙarshen shekara.
Alhaji Idris ya kuma ce za a riƙa ɗaukar wasu daga cikin mahalarta taron don ba su horaswa ta musamman a kan fasahohin zamani ciki har ilimin ƙirƙirarriyar fasaha wato artificial intelligence, wanda ma’aikatar za ta shirya. Ya ƙara da cewa makamancin wannan taro za a shirya shi ga ‘yan jarida daga Kudancin Najeriya a nan gaba.
Ministan ya shawarci’ yan jaridar na Soshiyal Midiya su nisanta kansu da labarun bogi domin inganta aikin su.