Minista Ya Sake Jaddada Ƙudirin Sabunta Kayan Aikin Watsa Labarai Na Gwamnati

 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta sabuntawa da kuma inganta dukkanin kayan aikin watsa labarai na gwamnati, a wani ɓangare na ƙoƙarin ta na gyara fagen yaɗa labarai a Nijeriya.

Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya faɗa a cikin takarda ga manema labarai cewa Ministan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin da yake jawabi a Zauren Taron Manema Labarai da Ministoci na Shekarar 2025, karo na shida, wanda aka gudanar a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa da ke Abuja.

Ministan, wanda bai daɗe da dawowa daga Babban Taro Da Bita na Ƙungiyar Masu Watsa Labarai ta Ƙasa (NAB) da aka gudanar a birnin Las Vegas na ƙasar Amurka ba, ya ce taron – mai taken “Fasaha, Madosa, Makoma” – ya ƙunshi musayar ra’ayoyi daga ƙwararru a fannin fasaha da watsa labarai daga sassa daban-daban na duniya.

Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa.
Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya.

Ya ce: “Ina sanar da ku waɗannan abubuwan ne domin jaddada ƙudirin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an samu cigaba mai ɗorewa a fannin watsa labarai a ƙasar nan.

“Wannan ne ma ya sanya muke gudanar da irin wannan taron bita na ministoci, da kuma shirin ƙaddamar da Taron Tattaunawa da Jama’a a sassan ƙasar nan nan gaba kaɗan.”

Idris ya kuma bayyana halartar da ya yi a Taron Kasuwanci na Nijeriya da aka yi a birnin Paris, ƙasar Faransa, wanda kamfanin Business France ya shirya.

A gefen taron, Idris ya gana da manyan jami’an hukumar UNESCO domin ƙara inganta shirin kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai a birnin Abuja.

A cewar sa, wannan cibiyar za ta taimaka gaya wajen bunƙasa hazaƙar ‘yan jarida da kuma gina sahihin tsarin yaɗa labarai mai inganci a ƙasar nan.

Ya ce: “Cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa wurin ƙara ƙarfin gwiwa da ingancin aikin ‘yan jarida a Nijeriya.”

Idris ya ƙara da cewa shirye-shiryen da ake yi kamar wannan taron bita da kuma Taron Tattaunawa da Jama’a da ke tafe, yana daga cikin dabarun gwamnatin don ƙarfafa gaskiya, ƙarfafa tattaunawa tsakanin gwamnati da al’umma, da kuma ƙarfafa amincewa a tsakanin ɓangarorin biyu.

A yayin taron, Ministan Wutar Lantarki, Cif Adebayo Adelabu, ya yi bayani kan matakan da ake ɗauka don gyara ɓangaren wutar lantarki domin tallafa wa shirin gwamnati na bunƙasa masana’antu da tabbatar da isasshiyar wutar lantarki ga ‘yan Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SUBSCRIBE US

It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution

Copyright BlazeThemes. 2023