Babbar kotun majistare da ke yankin Wuse 2, Abuja, ta yanke wa wani Farfesa mai suna Jide Josiah Jisos hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin yi wa ‘yarsa jarrabawa a lokacin yin jarrabawar gama-gari ta JAMB a 2019.
Babban Alkali Folashade Oyekan ne ya yanke hukuncin a ranar 24 ga Oktoba, 2024.
Jami’ai daga hukumar shigar da kara da kuma hukumar JAMB ne suka kama Jisos a lokacin da yake sa ido a jarrabawar ta UTME a Brix Academy da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa daga jami’in yada labarai na JAMB, Dr. Fabian Benjamin, Jisos ya gabatar da kansa a matsayin wakilin wata kungiya mai zaman kanta (NGO) da nufin sa ido kan jarrabawar.
An fallasa dabararsa ne a lokacin da shugaban tawagar sa ido ya yi masa tambayoyi, inda ya nemi karin haske game da kasancewarsa a wajen.
Yayin da ya kasa bayar da gamsassun amsoshi, sai aka gano dabararsa, kuma nan take aka kama shi tare aka mika shi ga jami’an tsaro domin ci gaba da bincike.
A lokacin da ake yi masa tambayoyi, Jisos ya yarda cewa ba shi da wata alaka da wata kungiya mai zaman kanta kuma ya shiga dakin jarrabawar ne domin ya taimaka wa ‘yarsa wajen rubuta jarrabawar.
Baya ga hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, an ba shi zabin biyan tarar Naira 100,000.