HASASHE – Halima Abdullahi k Mashi

page 1

 

Halifa ya kalli Abokan sa dake ta daga dinkin Sulaiman daya daga cikin su , suna ta farin cikin gabatowar bikin Halifan wanda ya rage saura kwana tara, dai dai lokacin ma ‘yan kai lefe suna can gidan su Bilki amarya.

 

Kati za su  kasaftawa wanda za su fara rabon shi nan da kwana uku.

Wayar Halifa ta yi kara, cikin zumudi ya ciro da zaton amaryar ce dan yana ta dakon kiranta.

Hafsi ce yariyar Antysa wadda tana cikin yan rakiyar kai lefe.
Ya daga da tambaya. •Hafsi har kun fito?” Muryoyi ya ji suna tashi kamar ana rigima. Ta katse shi da fadin “Uncle Halifa wallahi sun raina kayan nan. Kuma wai ba a sako kaya sa lalle ba,  Baba ta fada musu yanzu ba a yin kayan sa lalle tunda turare ake fesawa sai suka ce su har yau suna rike da wannan al adar. Wai atamfa goma leshi biyar shadda biyu wannan harkar tsiya har ina…

“Me Umman su  Bilki tace?  Halifa ya katse Hafsi.

Tace “Cewa ta yi Allah ya so ba ta gayyato kawayanta gurin kabar lefen ba da ta sha kunya.
Wai a sasu kasan gado gara ace ba a yi lefen ba, kuma wai kayan tukwicin ba za a bamu ba wai tunda mun sha fiya wata a mai da leman  da cincin ba kuma zata bada ko nera ba.”

Halifa Ya sauke wata wawuyar ajiyar zuciya sannan yace ina Bilkisu? Tace “Gata can tana kuka.” Yace kai mata wayar, karki kashe.
Yana jiyo muryar kanwar mahaifiyar shi Baba tana cewa mun zata kayan nan al adace kuma kowa yana yin daidai karfin sane.

Yaji lokacin da Bilkisu take cewa  Hafsi bazan amshi  wayar  sa ba, sai kuma tace kawo dai. ya ji daya daga gare ni.
Ta shiga zazzaga masa bala’ i tana fadin ya bata mamaki ashe duk kiran sun shiga kasuwa  ya yi aike Dubai da yake yi iya tsiyar da ya siya kenan akwati uku da gana masgo. Wallahi Halifa ka bani kunya.

Halifa ya share zufar fuskarshi ya kalli abokan shi da suka yi cirko cirko cikin sanyin murya yace Bilki kin raina wadannan kayan?
Cike da gadara tace “Na raina su Halifa!! Yace kenan dan kaya ki ke sona? Tace “Halifa zan fison a ce ba a kawo ba sam!” Yace shike nan ku basu kayan su maido min. Tace. “Yanzu kuwa har katin ka da ka bada.
Bai kuma cewa komai ba ya kashe. Take ya soma kiran layin Baba.
Ta daga yace Baba ku dawo da kayan kawai,. Baba  tace “Bari mu gani ko za a samu maslaha. Megidan muke jira . ”   Yace Baba kawai ku rabu da su ku taho. Ta katse wayar tare fadin zan kira ka ga Antyn ka tana kira na.”

Ya dubi. Abokan sa da suka cika da al’ajabi yace ku kona katunan nan Wallahi na fasa.

Suka fito suka zauna a dakalin kofar gidansu Sulaiman suna bashi baki tare da shawarin yadda ya kamata a yi. Bashir ne kadai ke goyon bayan shi dan yace ko shine fasawa zai yi.

Da idon ya ke binsu amma ba lallai yana fahimtar inda suka dosa ba. Zuciyar shi da kwakwalwar shi suna maimaita masa zafafan kalaman Bilki. Wanda kullum  ta ke nuna mishi in bashi bazata  iya rayuwa ba. Gefe kuma yana tuna kudin da Abokan shi suka kashe na game da shirin fati wanda Bilkin ta matsa sai anyi. Iya Hall dubu dari uku  su ka biya banda sauran abubuwa.

Siririyar murya ta katse masa tunani, sannunku Yaya Sulaiman. Halifa baya ciikin wadanda suka amsa, amma ya bita da kallo bazata fi shekara sha bakwai zuwa takwas ba, sanye da kayan islamiya wadan da suka jeme suka kode kwadat.
Sai yaji bakın shi ya furta cewa ke zo. Ta dawo baya ta ce “Gani.” Ga zaton ta aiken ta zasu yi. Halifa yace zaki aure ni? Ta ce “Mene?” Yace nasan kinji amma bari in maimaita kuma ki bani amsa zaki aureni?
Tayi yar dariya zata wuce, yace na yi miki kama da wanda zai miki wasa? Su Sulaiman sun kasa magana dan mamaki. Domin dai sun san gaske Halifa baya cikin yanayin da zai yi wasa, ko da dama ba mai wasan bane.
Ta daga kai alamar eh. Halifa ya kalli Sulaiman “ina ne gidan su?” Sulaiman yace Asiya ki shiga gida. Sannan ya dubi Halifa “Dan Allah ka nutsu ka bari a sasanta waccan maganar yarinya nan kamar kanwata take kaga gidan su da namu katanga ta raba, ba zan so wata matsala ta same ta ba.

Halifa yace wallahi ita zan aura, ka wai sanar dani ina Baban ta?
Sulaiman yace Halifa wannan halayyar ta ka ta saurin yanke hükünci kayi kokarin rabuwa da ita, Baban ta yana cikin gida yana fama da ciwon suger kafa daya ma gare shi an cire dayar, dan Allah kar ka sa su a damuwa. Yarinyar nan ga wurin da take tuyar awara can, yayar ta Sadiya bazawara ce mijinta ya mutu bara tana gidan da yaranta biyu , aikatau take zuwa gidan masu hali kusan su ke rike da gidan. Namijin su karamine tallar fiya wata yake zuwa a danja,  tuni sun dai na boko sai islamiya. Na san ba irin matar da ka ke so bace Asiya.

Halifa ya mike, muje kamin sallama da Baban su kawai na canza ra ayi irin wadda nake son yar gayu yar  birni  wayayya baga shi kana gani abinda suka min ba. Usman ya dagawa Sulaiman hannu tare da fadin kar ka hana shi kaje kawai.

A soron gidan suka zauna a tabarma kallo daya zaka yi wa Baban ka tabbatar yana jin jiki. Bayan sun yi masa sannu, sai Halifa ya fara magana.
Baba dama ni ne nake son auren.. ya kalli Sulaiman dan baima san sunan ta ba. Sulaiman yace  “Asiya ya gani yake so. Halifa ya amshe da fadin kuma Baba ina son nan da kwana tara in zai yiwu,aure na za ayi suka raina lefen maganar ta watse, in har ka amince min yanzu za a kawo kayan nan gidan nan Baba.”

Baban su Asiya ya ya yi dan tari, murya can kasa yace “Samari , ba a saurin yanke hukunci gaggawa wani lokacin daga shedan take, hakika naji dadi har da ka ga ‘ya ta ka ce kana so, amma ita tana son ka? Wannan abu na farko da ya kamata in sani. “. Halifa ya yi karaf yace  a kira ta a tabbatar Baba amma ni ta fada min cewa ta amince.

Ya kalli Sulaiman “Leka kace. Asiya ta zo” Daidai lokacin tana ba Sadiya da Innar su labarin yadda su kayi da abokin Sulaiman kuma shine wanda ya yi sallama da Baba. Innarsu duk sai taji tsoro ya kamata domin bata taba ganin irin wannan abu ba.
Sadiya kuwa cewa  ta yi  Allah ya sa ya zama alkhairi tasan Sulaiman ba zai cutar da su ba.

Kiran da Sulaiman ya kwado cikin gidan shine ya sa hantar cikin Asiya ta juya har taji tana jin bayan gida. Innarsu tace “kije amma karki ce kin yarda kice wasa ki ke yi. Asiya tace to.
Ta tsuguna Baba yace Asiya kin yarda cewa zaki auri wannan yaron abokin Sulaiman? Ta daga ido ta kalle su, baza ta iya tantance waye a cikin su yanzun ba.
Ta sake sunkuyar da kai sai tace daga kai alamar eh ta kasa yin yadda Innarsu ta fada mata. Baba yace mata kin tabbata?
Ta sake daga kai, yace ta koma ciki,

Ya dube su. “Sulaiman tunda Asiya ta yarda kuma abokinka ne gaka ga shi ni bansan shi ba amma na sanka, duk wani bincike kai ne dama zan sa a gaba dan Asiya kanwarka ce, ina son ka bani wani tabbaci game da shi.”

Sulaiman yace Baba bansan wani mutum mai saukin kai kamar  Halifa ba, sannan yana da ilmi duka biyu yana da sana’a kuma yana da a kida ahlissuna ne, ga ibada. Tare mukayi karatun sakandire mu hudun nan duk cikinmu ya fimu sukuni amma komai tare muke, ya yi ta taimaka mana a makaranta kuma har zuwa yanzu,  bai canza mu ba. “

Baban Asiya yace “To shike nan amma wani hanzari ba gudu ba, ni dai kaga a yadda nake  da ina da hali ma yanzu ace ina gadon Asibiti dan haka bani da sukunin aurar da ita a yanzu. Sai dai a sa lokaci Muga abinda Allah zai yi.” Halifa yace me cece damuwar Baba?  Baban Asiya yace “kayan daki mana na yarta kuma kwanaki da jikina ya motsa lokacin da za a yanke kafar nan aka sai da su da sai a kaimata duk da suma ba na zamani bane. Itama lokacin sasantawa mukayi da yaron suka kawo kudi madadin lefe ya yi mata dan kala biyu na fitar biki muka hada da dan abinda ke hannunmu a ka rufa asiri.
Kai kuma gashi da lefanka a hannu bare a yi hakan.

Halifa ya gyara zama Baba ni dai yarinya nake so ba kaya ba. In katifa ta samu ko da sadakin ta ne ku sai mata Allah shine mai yalwatawa. Dadi ya rife Baba yace “To yaro na amince, sai dai ina son ka kawo magabatan ka. “

Halifa ya ce za su zo amma dai yau ina son ku karbi kayan ku ajiye gobe zan kawo su. Baba ya amince.

Suka fito suna mamki  lamari kamar wasa yana neman zama gaske.
Halifa ya daga kiran da ke ta shigo wa  wayar sa yana katsewa lokacin da suke magana da Baban Asiya. Baba ce, tace ina ta kira kazo mu tafi an sasanta da Abban su ya zo akan za a karo wası abubuwan kuma za a kawo kayan sa lalle Antyn ka ta amince akan haka. “

Halifa ya yi wata yar dariya takaici kamar yarda ya zata shima Abban su Bilki jeka na yi ka ne. Yace Amma kuna gidan har yanzu? Tace e sun bamu kayan tukwaicin. “. Yace ku dai jirani a gidan.
Ya dubi Bashir zo muje ku kuma ku jiramu a nan. Suka fita a layin zuwa inda ya aje mota kasancewar layin in an shigo da mota sai dai a fita ta baya to baya shigowa da mota.

Suna isa yace Bashir kayan nan zamu amso fa. Bashir yace “Shine daidai fa. “ Suka sallama Hafsi ta fito Tana ta tura baki tana fadin”Wallahi Uncle duk da haka suna ta yarda magana“

Yace kuje ke da Bashir ku kwaso min kayana.
Baba tana ‘a’a yace kiyi hakuri wani gurin za a kai kayan. Abinda wani ya raina shi wani ke farin ciki da şamın shi.

Umman su Bilki su ka ce ya haka ?  Bashir yace za a canza ne sai a hado da karin. Suka sa kaya a mota Halifa yace a maida ruwan da lemon da cincin din.
Bashir yace baza a maida ba, kamar yadda na tabbatar baza su maido maka da kudin auren ka ba, banda hidin dimu da kayi mata.

Kamar wasa sai ga kaya ankai gidan su Asiya makota suka shigo aka amsa cikin girmamawa ba kayan tukwici amma Innar su Asiya ta kebe da Umman su Sulaiman ta ari dubu biyar ta basu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SUBSCRIBE US

It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution

Copyright BlazeThemes. 2023