Gwamnatin Nijeriya ta bayyana ƙudirin ta na amfani da Ƙirƙirarrar Basira (AI) a aikin jarida cikin ɗa’a, tare da mayar da hankali kan ‘yancin faɗin albarkacin baki, bin ƙa’idojin aikin jarida da kuma koyar da jama’a ilimin kafafen watsa labarai.
An ƙarfafa wannan ƙudiri ne a taron bikin Ranar ‘Yancin Jarida ta Duniya na shekarar 2025, wanda aka gudanar a otal ɗin Sheraton da ke Abuja a ranar Juma’a, ƙarƙashin jagorancin Konrad Adenauer Stiftung (KAS) da Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙiren Jarida da Cigaba (CJID).
Taken taron shi ne: “Rahoto a Sabuwar Duniya – Tasirin AI Kan ‘Yancin Jarida da Kafafen Yaɗa Labarai,” inda aka tattauna yadda Ƙirƙirar Basira take sauya salon aikin jarida da ƙalubalen da ke tattare da hakan.
A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai.
Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da rahoto, da nazarin bayanai da gudanar da bincike, yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da wannan sabuwar fasahar cikin hankali da bin ƙa’idoji.
Ya ce: “A yayin da muke rungumar aikin jarida da fasahar AI, dole ne mu tabbatar da cewa ba za a tauye ‘yancin jarida ba, illa ma a ƙara ƙarfafa shi.”
Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya za ta kafa Cibiyar Ilimin Kafafen Watsa Labarai ta UNESCO a Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN), inda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya riga ya amince da kuɗin kafa cibiyar.
Ana sa ran wannan cibiyar za ta kasance cibiyar ƙasa da ƙasa da za ta inganta aikace-aikacen kafafen watsa labarai cikin gaskiya da tunani mai zurfi a fannin dijital.
Haka kuma, ya bayyana cewa Nijeriya tana kan hanyar ƙaddamar da tsarin dokar ƙasa kan amfani da AI a cikin aikin jarida.
Wannan tsari zai ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire amma ba tare da tauye ‘yancin jarida ko karya ƙa’idojin aikin ba.
Idris ya buƙaci haɗin gwiwa tsakanin ‘yan jarida, da masana fasaha, da kafafen yaɗa labarai, da ‘yan siyasa da ƙungiyoyin farar hula domin samar da ƙa’idojin amfani da AI, da koyar da sababbin dabaru, da tabbatar da gaskiya, da kuma faɗakar da al’umma.
A nata jawabin, Marija Peran, wakiliyar KAS a Nijeriya, ta jaddada irin damar da AI ke bayarwa ga aikin jarida, tare da yin kashedi kan haɗurran da ke tattare da hakan.
Ta ce: “Yana da muhimmanci mu kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai a duk duniya, musamman yanzu da AI ke ƙara shiga aikin jarida.
“A matsayin ta na ƙungiya mai kishin dimokiraɗiyya da doka da oda, KAS tana tare da kafafen yaɗa labarai wajen fuskantar wannan sabon yanayi.”
Taron ya samu halartar mutane daban-daban, ciki har da Shugaban Kwamitin Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Majalisar Wakilai, Honarable Akintunde Rotimi Jr.; da wakilan kafafen yaɗa labarai, da ƙungiyoyin farar hula da kuma abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.