Ganduje ya maida martani

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani mai zafi ga Buba Galadima bisa kalaman da ya yi na cewa Ganduje ya rasa tasirin siyasa.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala, ya fitar, Ganduje ya bayyana Galadima a matsayin “ɗan siyasa da ya mutu, aka yi watsi da shi, kuma yana cikin fargaba” wanda ba shi da wani tasiri a siyasar Najeriya.

Okpala ya ce Galadima ba shi da kwarjini, kuma yana da tarihin sauya ra’ayi akai-akai don amfanin kansa.

Ya tunatar da jama’a cewa Galadima ya kasance cikin tawagar Buhari a baya amma ya kasa taimaka mata wajen cin zaɓe a lokacin.

Ya yaba wa nasarorin Ganduje a lokacin da yake gwamnan Jihar Kano, yana mai cewa ayyukansa har yanzu suna bayyana kuma yana da farin jini a tsakanin al’umma-Albarka Radio FM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SUBSCRIBE US

It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution

Copyright BlazeThemes. 2023