Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan rasuwar dattijo ɗan kishin ƙasa kuma tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Tarayya, wato Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru 97. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana Cif Clark […]
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ƙasashen duniya da su sauƙaƙa tsarin ba da biza ga kamfanonin Nijeriya da ke ƙoƙarin kafa masana’antu da kasuwanci a ƙetare. Ministan ya yi wannan kira ne a Addis Ababa, babban birnin Habasha, a ranar Lahadi yayin da yake wakiltar Shugaban Ƙasa […]
A wannan rana ta Lahadi, na wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ganawa da shugabannin ƙungiyar jama’ar Nijeriya mazauna ƙasar Habasha. Wannan dama ce da muka samu muka ji matsalolin su tare kuma da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta sa hannu a lamarin. Abu mafi muhimmanci shi ne, sun yi murnar jin […]
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗau hoto tare da sauran Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatoci a wajen Zama na 38 na Taron Babbar Majalisar Ƙungiyar Haɗa Kan Afrika (AU) a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha a ranar wannan Asabar ɗin. Hoto na 2: Shugaba Ahmed Tinubu tare da sauran Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatoci suna […]
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Ba’amurken nan Mista Tigran Gambaryan ya yi kan wasu jami’an gwamnatin Nijeriya, tana mai bayyana shi a matsayin ƙarya da yaudara. Gambaryan dai jami’in kamfanin Binance ne daga Amurka, wanda hukumar EFCC ta gurfanar a Nijeriya a 2024 bisa almundahanar kuɗi. Kwanan nan ne Gambaryan ya fito ya […]
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga gidajen rediyo a faɗin Nijeriya da su yi amfani da kafafen su wajen ilimantar da jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa. A cikin wata sanarwa da ya bayar domin bikin Ranar Rediyo ta Duniya ta 2025, wadda ake gudanarwa […]
Gwamnatin Tarayya ta jaddada ƙudirin ta na rage farashin kayan abinci ta hanyar zuba jari mai yawa a fannin noma. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin wani taron manema labarai da ya buɗe zaman bayar da rahoton ayyukan ministoci na […]
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Hukumar Sayen Kayayyaki ta Ƙasa (BPP) kan ƙoƙarin ta na inganta gaskiya da riƙon amana a wajen sayen kayayyaki da bayar da kwangiloli. A wata ganawa da ya yi a Abuja a ranar Alhamis tare da Babban Daraktan BPP, Dakta Adebowale […]
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Nijeriya ta samu goyon bayan ƙasashe bakwai tare da alƙawuran ƙasashe 20 domin a kafa Cibiyar Koyar da Ilimin Yaɗa Labarai ta Duniya (IMILI) ta hukumar UNESCO. Ita da UNESCO, ita ce Hukumar Ilimi da Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin […]
A bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, an kai waɗanda suka jikkata a haɗarin fashewar tankar man fetur a Suleja zuwa manyan asibitoci don su samu kulawa ta musamman. A cikin wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris […]
It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution