Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ba da cikakken goyon baya ga samar da wani shirin fim mai nuna tarihin shekaru 25 na mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Majalisar Tuntuɓa ta Jam’iyyun […]
Gwamnatin Nijeriya za ta yi amfani da damar da ta samu ta halartar Taron Kasuwanci na Faransa da ke tafe a birnin Paris don bayyana irin cigaban tattalin arzikin da aka samu ƙarƙashin shugabancin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, a cewar Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris.ki Ministan ya bayyana hakan […]
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Ƙungiyar Masana Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) murna kan samun damar karɓar baƙuncin Taron Hulɗa da Jama’a na Duniya (World Public Relations Forum, WPRF) na shekarar 2026. Sanarwar ta zo ne yayin wata ziyarar girmamawa da Shugaban NIPR, Dakta Ike Neliaku, […]
Gwamnatin Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin fahimtar juna guda biyu da aka rattaba wa hannu tsakanin Hukumar Watsa Labarai ta ƙasar Chana (China Media Group) da Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN) a Taron Haɗin Gwiwa tsakanin Chana da Afrika (FOCAC) wanda aka gudanar a birnin Beijing. […]
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗi na 2025 a matsayin wata muhimmiyar taswira ta ƙarfafa tattalin arziki, daidaito na zamantakewa, da cigaban ƙasa. Da yake jawabi a Taron Manema Labarai na Ministoci karo na uku na shekarar 2025 a Cibiyar Yaɗa Labarai ta Ƙasa da ke […]
A daren jiya Allah ya ɗauki ran Hajiya Hauwa, surukar Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris. Mahaifiyar maiɗakin Ministan ta rasu ne sakamakon rashin lafiya, tana da shekaru 70 a duniya. Mataimaki na Musamman ga Ministan, Hon. Saidu Enagi, ya bayyana cewa za a yi mata jana’iza a Babban Masallacin […]
Mai girma Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya kai masa ziyarar aiki a ofishin sa a Abuja.
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Gwamna Bago murnar cika shekara 51 Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umar Bago, murnar cikar sa shekara 51 a duniya. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Idris ya yaba wa gwamnan bisa shugabancin sa […]
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fara zagaye na biyu na Zauren Tattaunawa na Ministoci, inda Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Eshiokpekha Momoh, da Ƙaramin Ministan sa, Alhaji Uba Maigari Ahmadu, suka gabatar da jawabai kan ayyukan ma’aikatun su. Da yake gabatar da jawabin […]
Ministocin gwamnatin Tinubu za su fara gabatar da ayyukan da suka yi ko suka sa a gaba a Tarukan Manema Labarai na Ministoci na shekarar 2025 a ranar Juma’a, mai zuwa, 21 ga Fabrairu. Ma’aikatar Yaɗa da Wayar da Kai ce ta ba bayyana hakan, ta ce za a fara taron da ƙarfe 11 […]
It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution