Wakar Ambaliya

A daminar bana, Allah Ya jarabci sassan Najeriya da ambaliya, inda a makon nan ruwa ya mamaye kusan dukkan birnin Maiduguri. An yi asarar dukiya da ta rayuka. Khalid Imam ya rubuta wannan waƙe, domin jajantawa.

°°°°°°°

 

 

Ambaliya

Dubi dai ambaliyar, nan,

Ta share Shira da Buji,

Gwaram da Gadau Katagum

Je Buskuri ɗan uwana.

Yau ba hanya ta mota,

Ruwa duka ya malale.

 

Dorina ga naki cinye,

Ko’ina ka bi babu hanya,

Gonakin da yawan mutane,

Gidaje kasuwanni,

Ruwa ya lamushe su,

Masu mulki ba ruwansu.

 

Ruwa yau ya ci Borno,

Har fadar Shehu namu,

Ruwan ambaliya yau,

Bai bar Zazzau ba can ma,

Wasu ma sassan Kano yau,

Ruwa duka ya malale.

 

A ƙasa in shugabanni,

Gwamnoni masu mulki,

Sata ce alƙiblarsu,

Don takaici cin amana,

Sai su bar lamarin mutane,

Su yi ta harkokin gabansu.

 

Da suna da kula da gaske,

Da suna kishin jiharsu,

Da ba su barin mutane,

A halin ha’ula’i,

Ruwa ya kai su bango,

Ya shaƙe kwalar wuyansu.

 

Sakaci ne ko mugunta,

Zai sa gwamna ya manta,

Cewa jama’ar jiharsa,

Ruwa na hallaka su,

Ya ƙi yin komai da kansa,

Tun da ba zaɓe ake ba.

 

Tun da ba zaɓe a gobe,

Da zai zo yai ta kamfen,

Ya yi ƙarya don a zaɓar,

Ai ta ma ambaliyar man,

Masu yin zaɓe ta shafa,

Shi yana ofis a zaune.

 

Dukiyar jama’ar jiharsa,

Ta amana bai kula ba,

Shi da sauran masu mulki,

Suna wawa a kullum,

Lamarin jama’a ko oho,

Wannan ai su ta shafa.

 

Don sun iya cin amana,

Shugaba na ƙasa yana ji,

An sanar masa shi da gwamna,

Cewa bana babu shakka,

Sauyin yanayi da gaske,

Tarko yai wa mutane.

_______________

© Khalid Imam

Satumba, 2024

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SUBSCRIBE US

It is a long established fact that a reader will be distracted by the readable content of a page when looking at its layout. The point of using Lorem Ipsum is that it has a more-or-less normal distribution

Copyright BlazeThemes. 2023