An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942, a garin Daura da ke jihar Katsina. Muhammadu Buhari shi ne ɗa na 23 a wajen mahaifinsa Malam Harɗo Adamu wanda ya rasu lokacin da Buharin yake ɗan shekara huɗu.
Muhammadu Buhari ya taso a garin Daura, kuma ya kasance ɗaya daga cikin ‘ya’yan mahaifinsa, Mallam Hardo Adamu, wanda makiyayi ne. Ya fara karatun allo da karatun boko a makarantar firamare ta Daura, sannan ya cigaba da karatu a Katsina Provincial Secondary School (yanzu Government College, Katsina).
Gwagwarmayarsa a Aikin Soja
Bayan kammala sakandare, ya shiga rundunar sojin Najeriya a shekarar 1961. Ya karɓi horo a makarantu daban-daban na soja a Najeriya da kasashen waje, ciki har da Sandhurst Military Academy a Ingila. Buhari ya taka rawar gani a lokacin yakin basasa na Najeriya (1967–1970), inda ya rike mukamai daban-daban a cikin rundunar soja.
Shugaban Mulkin Soja (1983–1985)
A ranar 31 ga Disamba, 1983, Buhari ya jagoranci juyin mulki da ya kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya ta Alhaji Shehu Shagari. Ya zama Shugaban Ƙasa na mulkin soja daga 1983 zuwa 1985. Gwamnatinsa ta shahara da yaki da rashawa da cin hanci (war against indiscipline), amma an zargeta da take hakkin dan Adam da tsauraran matakai.
A ranar 27 ga Agusta, 1985, wani soja kuma abokin aikinsa, Janar Ibrahim Babangida, ya kifar da shi ta hanyar juyin mulki.
Hawan Mulki a Demokradiyya (2015–2023)
Bayan shafe shekaru da dama a bayan fage, Buhari ya shiga siyasa. Ya tsaya takara a shekarun 2003, 2007, da 2011, amma bai yi nasara ba. A karo na huɗu, ya tsaya takara a shekarar 2015 karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) inda ya kayar da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan. Wannan shine karon farko da shugaban Najeriya mai ci ya fadi zabe.
Ya sake lashe zabe a 2019 kuma ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu a 29 ga Mayu, 2023.
Ya Rasu a Ranar 13 ga watan Yulin da Muke ciki na Shekarar 2025.
Allah Ya gafarta Amin.
Follow 👉 Ashir Mai jama’a sokoto