Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun ƙaruwar aikata laifuka da damfara ta Intanet a yammacin Afrika
Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana damuwar a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumarsa ya fitar.
Ministan ya yi zargin cewar masu aikata laifin ta Intanet sun aikata hakan a kan ‘yan Nijeriya, ta hanyar yi musu romon-baka.
Sai dai masana harkokin sadarwar a Nijeirya na ganin akwai sakacin hukumomin ƙasashen waje, wajen aiwatar da dokoki da ke bai wa hukumomin da ke sanya idanu damar yin aikin da suka dace don magance wannan matsala.
Wannan na zuwa ne bayan asarar kuɗi da ’yan Nijeriya suka takfa a wani tsarin zuba jari mai suna CryptoBank Exchange wanda aka fi sani da CBEX ya ja hankali a ƙasar, musamman a kafofin sadarwa.
Wannan matsalar ta zo ne a daidai lokacin da ’yan ƙasar suke ci gaba da ƙorafi kan tsadar rayuwa da rashin kuɗi, wanda ya biyo bayan janye tallafin man fetur da karyewar darajar naira.
Rahotanni sun ce kuɗin da ’yan Naieriya suka yi asara a tsarin na CBEX sun haura naira tiriliyan ɗaya, wanda hakan ya sa wasu suke mamakin yadda ƴan ƙasar suka iya tara maƙudan kuɗi haka cikin ƙanƙanin lokaci.
Tuni dai Hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar ta sanar da fara gudanar da bincike kan lamarin.