Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar kaɗuwarsa bisa rasuwar babban malamin addinin Islama na garin Zariya, Sheikh Mainasara Liman Habibi.
Sheikh Habibi ya rasu a karshen makon da ya gabata yana da shekaru 67.
A lokacin rayuwarsa, malamin ya kasance shugaban masu wa’azi na kungiyar Fityanul Islam ta kasa wadda kungiya ce ta ‘yan uwa musulmi ta Tijjaniyya.
A cewar Shugaba Tinubu; Musulmai za su rika tunawa da Sheikh Habibi a matsayin jajirtaccen malami kuma mai himma wanda ya inganta ilimin addinin Musulunci da kuma yi wa bil’adama hidima.
Shugaban ya ƙara da cewa Sheikh Habibi ya yi amfani da wa’azinsa wajen yin kira ga zaman lafiya da haƙuri da juna, kana da hadin kan jama’a maimakon rarrabuwar kawuna.
Shugaba Tinubu ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Kaduna, da ma masarautar Zazzau da kuma ‘yan uwa Tijjaniyya a duk fadin Najeriya bisa wannan rashi da suka yi.
Shugaba Tinubu ya yi wa Sheikh Habibi addu’a, tare da rokon Allah ya jikan Malamin da gafara.
Bayo Onanuga
Mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan dabarun yada labarai
Afrilu 28, 2025