Fadar Shugaban Kasa ta yi kira ga yan adawa da su daina ɗora laifin gazawar su ga Gwamnati, ta kuma bayyana cewa demokaradiyya na nan daram a Najeriya, babu wani yunƙuri na hana ‘yancin siyasa ko wani yunƙuri na kafa jam’iyya ɗaya tilo a Najeriya.
A wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan yaɗa labarai ya fitar, gwamnatin ta ce korafe-korafen da wasu ’yan adawa da masu kare hakkin ɗan Adam ke yi na cewa ana kokarin karya demokaradiyya, batu ne da ba shi da tushe balle makama.
Sanarwar ta bayyana cewa yan adawa sun shiga ruɗani ne tun bayan sauya shekar da Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, da Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Dr Ifeanyi Okowa, da wasu manyan ’yan siyasa daga jihohin Delta da Rivers suka yi zuwa jam’iyyar APC.
Fadar Shugaban Kasa ta kuma musanta zargin cewa ana amfani da tsoro, cin hanci ko tilas wajen karkato ra’ayin masu sauya shekar, tana mai cewa ‘yancin zaɓin jam’iyya hakki ne na kowane ɗan kasa. Ta kara da cewa waɗanda ke kuka da sauya shekar suna fatan jam’iyyar APC ta afka rikici ne domin su samu damar cin gajiyar rikicin.
Sanarwar ta jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu ya kasance ɗan rajin demokaradiyya tun zamanin gwagwarmaya, kuma yana ci gaba da gina harsashin tabbatar da demokaradiyya a Najeriya. Ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su guji jin maganganu marasa tushe daga masu yaɗa ƙarairayi daga yan adawa.
A ƙarshe, sanarwar ta yabawa Shugaba Tinubu da Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Ganduje, bisa ƙoƙarinsu na sa jam’iyyar ta zama abar so da jan hankalin ’yan kasa.