Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware tsabar kuɗi har Naira Biliyan 15 ga Hukumar bayar da agajin gaggawa ta tarayya (NEMA) don shirye-shiryen tunkarar ambaliyar ruwan da ka-iya faruwa a daminar bana.
Haka kuma Mataimakin Shugaban ƙasar ya bayyana cewa gwamnatin ta kammala shirye-shiryen da suka wajaba wajen ƙaddamar da wani shiri da zai daidaita farashin kayan abinci da habbaka harkar noma don inganta tattalin arzikin ƙasa (NAPM).
Shettima ya furta waɗannan kalamai ne jiya Juma’a a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja yayin taron da ya gudanar da kwamitin shugaban ƙasa da zai kula da harkokin abinci. Inda ya ce wannan shiri zai haɗa hannu da gwamnatoci wajen ingantawa tare da samar da abinci.