*
A yau Lahadi ne wakilan al’umma mazaunan gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT) suka kai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ziyara domin gaisuwar Sallah a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, shi ne ya jagoranci ziyarar.
Ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaron Ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, da shi kan sa, da sauran jami’an gwamnati sun halarci zaman ziyarar.
Idris ya miƙa saƙon gaisuwar Sallah ga dukkan al’ummar Musulmin Nijeriya da na duniya baki ɗaya.