A ci gaba da nuna alhininta kan rasuwar Marigayi Alh Aminu Dantata, Wata tawagar gwamnatin tarayya ƙarƙashin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ta isa jahar Kano don ci gaba da zaman makokin Marigayin.
Tawagar, wadda ta kunshi manyan Jami’an gwamnati kamar mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia; Mai bai wa shugaban kasa shawara kan ayyuka na kasa, Dr. Aliyu Modibbo; da kuma tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Dr. Mohammed Bello Adoke sun sami tarba daga gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, tare da manyan jami’an gwamnatin jahar inda suka dunguma zuwa gidan Marigayin.
Mataimakin shugaban kasar ya gabatar da addu’ar Allah Ya jaddada Rahma ga Marigayin tare da tabbatar wa da iyalan marigayin cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na tare da su a wannan lokaci na jumami da ma bayansa.